Babban shafi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Star Ouro 8bits.png
Muƙalar mu a yau
Sunan Muhammadu Bello
Muhammed Bello (Larabci: محمد بلو) Shi ne sarki Sarkin Musulmi na biyu. Ya yi mulki daga shekara ta 1817 har zuwa shekara ta 1837. Ya kasance marubucin tarihi ne wanda ke da Ilimin addinin Musulunci. Ɗan Usman dan Fodio ne kuma mai masa hidima, wanda shi ne ya kafa Daular Sokoto kuma shi ne Sultan (Sarkin Musulmi) na farko. Lokacin mulkinsa, ya ƙarfafa da'awar yada Musulunci a dukkanin yankunan Kasar Hausa, da tsarin karantar da mata da maza, da kuma kafa kotunan Musulunci, Ya rasu a watan Octobar 25, shekarar 1837, kaninsa Abu Bakar Atiku ne ya gaje shi, daga nan sai dansa mai suna Ali Babba bin Bello ya gaji sarautar a gurin Abubakar Atiku.
Wikipedia:A rana irin ta yau 2 ga Maris, A rana irin ta yau

Yau 27 ga watan Yuli na 2022 Ga wasu muhimman abubuwa na tarihi da suka faru a wannan rana.

  • 1996 - A rana irin ta yau a shekara ta 1996 wani bututun mai ya fashe a filin shakatawa na Olympic Centennial da ke birnin Atlanta na kasar Georgia, inda ya kashe mutum 1 tare da raunata mutane 111 a harin ta'addanci na farko da aka yi a gasar Olympics tun bayan gasar 1972 a birnin Munich na Yammacin Jamus.
  • 1953 - An rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da makamai da za ta kawo karshen yakin Koriya a P'anmunjŏm da ke tsakiyar Koriya.
  • 1919 - Rikici ya ɓalle a Chicago bayan da aka sace tare da ɓatar da wani matashi Bakar fata kuma aka nutsar da shi a tafkin Michigan saboda yin iyo a wani yanki da aka kebe don farar fata kaɗai
  • 1214 - A yakin Bouvines, Sarkin Faransa Philip II ya yi nasara a kan kawancen kasa da kasa karkashin jagorancin Sarkin Roma mai tsarki Otto IV.
  • 2012 - Sarauniya Elizabeth ta biyu a hukumance ta bude gasar Olympics ta lokacin bazara ta 2012 a London

Wannan dai shi ne karo na 3 da birnin Landan ke karɓar baƙuncin gasar wasanni ta ƙasa da ƙasa da dama. An kira bikin ne Isles of Wonder kuma Danny Boyle ne ya ba da umarni

  • 1985 - juyin mulki a Uganda Tito Lutwa Okello, wani hafsan sojan Uganda ya yi nasarar yin juyin mulki kan shugaba Milton Obote. Shugaban kasar mai ci Yoweri Museveni ya hambarar da shi bayan watanni 6.
Nuvola apps filetypes.svg Ko kun san...?
  • Kwale kwale mafi tsufa da aka taɓa ganowa a nahiyar Afrika, kuma na uku mafi tsufa a duniya shine wanda wani bafulatani ya gano a shekara ta 1987 a ƙyauyan Dunfuna dake ƙaramar hukumar Fume dake jihar Yobe.
  • A shekara ta 1967, shugaban Najeriya Yakubu Gowon ya raba shiyoyin Najeriya zuwa Jihohi goma sha biyu.
  • Ƙasar Thailand itace kawai ƙasar da turawa basu yiwa mulkin mallaka ba a yankin kudu maso gabashin Asiya.

Mutanen ƙasar Holand sune suka fi tsawo a duniya. Ƙasar Brazil itace tafi samar da lemu a duniya.

  • Tsohon shugaban Najeriya Janaral Murtala Mohammed shine ya kafa tubalin gina babban birnin Tarayyar Najeriya wato Abuja saboda babban birnin Nigeria a wancan lokacin wato Lagos yana fama da cunkoson jama'a. Ya zaɓi tawagar mutane bisa jagorancin mai shari'a Akinola Aguda wanda ya zaɓi Abuja a matsayin sabon gurin da za'a gina babban birnin Nigeria
  • Kashi ishirin da uku ne kawai na mutanen ƙasar New Zealand suke haihuwar sama da 'ya 'ya biyu.
  • Birnin Vatican itace ƙasa mafi ƙanƙanta a duniya, domin mutanen wannan ƙasar basu wuce dubu ɗaya ba.

Ƙasar Brazil itace tafi yawan tsirrai nau'uka mabanbanta, tana da nau'uka daban daban na tsirrai har 55,000.

  • Mutane da dama a sassan ƙasar Sin (China) suna cin ƙwari, wasu daga cikin ƙwarin da suka fi farin jini sune tsutsa da kunama.
  • Tsibirai 332 ne suka haɗu suka samar da ƙasar Fiji.
Coronavirus virion structure.svg
  • Jirgin dake zirga-zirga a hanyar Abuja zuwa Kaduna ya goce daga kan layin sa a garin Kuwa kusa da shiga babban birnin tarayyar Nigeria Abuja.
  • Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ajax ta kori kocinta Alfred Schreuder bayan gaza cin ko wasa ɗaya cikin bakwai da ya jagoranci ƙungiyar.
  • A Najeriya al'ummar ƙasar na cikin wani irin yanayi a yayin da wa'adin da gwamnatin ƙasar ta tanadar na dena amsar tsofaffin takardun kuɗin ƙasar na ₦200, ₦500, ₦1000
  • A Jihar Osun dake kudancin Nigeria, Kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta ayyana Oyetola a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan wanda aka gudanar a bara. Alƙalin kotun Mai Shari'a Tertsea Kume ita ta tabbatar da cewa tsohon gwamman ne ya ci zaɓen.
  • Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai na jam'iyyar PDP a mazaɓar Birnin Kebbi da Kalgo da Bunza da e Jihar Kebbi, Abba Muhammed Bello, ya rasu.

Zaka iya duba babban shafin English Wikipedia
Nuvola filesystems camera.png Hotan mu na yau

Hoton mu na wannan ranan

Waje ne da yake jan hankalin masu zuwa yawon buɗe ido a birnin Katsina.

Sautin mu na wannan ranan

Tamburan ban girma na Algaita

Problems playing this file? See media help.

Bidiyon mu na wannan ranan

Yayan masu mulkin gargajiya na Hausawa akan dawaki.

Wikimedia logo family complete 2009.svg Yan uwan Wikimedia
Wikimedia Foundation
Wikiquote-logo.svg Wikiqoute
Azanci
Wiktionary-logo-pt.png Wikitionary
Ƙamus
Wikinews-logo.svg Wikinews
Labarai
Wikisource Wikisource
Wikisource
Commons-logo.svg Commons
Fayiloli
Wikidata-logo.svg Wikidata
Wikidata
Wikibooks-logo.svg Wikibooks
Litattafai
Meta-Wiki Meta-Wiki
Meta
Wikipedia logo bronze.png Shafuka na musamman
Magana da Admin

• Domin magana da admin ka latsa wanna mashigin Admins na Hausa Wikipedia

Zauran Tattaunawa

Zauran TattaunawaShafin tattauna al'amuran sauya-sauyen babban shafi

Zauran taimako

Zauran Taimako

Shafin Tarihi na Hausa Wikipedia

Tsohon Babban ShafiShafukan kidiyaShafukan GasaShafukan furojet

Shafin kirkira da inganta mukaloli

Sababbin mukaloliMuƙaloli masu kyauMukalolin dake bukatar a inganta su

Shafin Goge Mukaloli

Mukaloli mara sa inganciGoge mukalaMukaloli marasa hujja

Yanda ake editin a Hausa Wikipedia

Tutorial a rubuceTotoriyal na bidiyoTotoriyal na PDF

Gyare-gyare

Lasisin amfaniKididdigan Hausa WikipediaBabban gargaɗiGame da Wikipedia