Halima Aden, mai ado da hijabi ta farko, ta bar masana'antar ƙawa a watan Nuwamba tana mai cewa hakan bai dace da tsarin addinin Musulinci ba. A wata hira ta musamman, ta bai wa wakiliyar BBC Sodaba Haidare cikakken labarin yadda ta zama abar koyi, da kuma yadda ta yanke shawarar barin harkar. Halima, mai shekara 23, tana zaune a St Cloud da ke jihar Minnesota, inda ta