Barka!

Babbar Ranar Tarjamar WordPress ta Duniya ta 2 Ranar 12 ga watan Nuwamba, 2016

Babbar Ranar Tarjamar WordPress ta Duniya na farko da akayi ya kayatar. Mun ji dadi sosai, kana bukin ya taimaka sosai wajen kawo mana sauyi mai ma’ana, a matsayin mu na wata kungiya ta duniya baki daya. Saboda haka ne ranar 12 ga watan Nuwamba zamu maimaita irin wancan aiki da mu kayi, kuma muna gayyatar kowa!

Me za muyi?

  • Ranakun taimakawa don tarjamar na kasa – muyi kokarin samun Karin masu taimakawa (a wancan lokacin daya gabata, mun sami fiye da 50, mu kara kaimi!)
  • Daga nesa muna son samun karin harsuna masu dama domin a taimaki wadanda ba zasu iya zuwa ba
    Zamu watsa komai har na tsawon sa’o’i 24 game da tarjama zuwa harsuna (localization) da fassara daga harsuna zuwa wasu harsunan (internationalization) (L10n da i18n).
  • Waye zai amfana?
  • Sabbin masu aikin tarjama don masu neman fassara WordPress zuwa harsunansu
  • Sabbi da kwararrun masu tace fassara – akwai bayanai masu amfani ga kowa wajen hada kwakkwaran tsarin yin fassara
  • Masu hada manhaja da ke bukatar wadanda zasu fassara ayyukansu – za’a koyar da kowa yadda ayyukan kungiyar tarjama ta WordPress yake, kana a sanar da kowa yadda ake hada masu fassara dukkan kayan manhaja da aka kirkira
  • Kwararrun masu hada manhaja dake bukatan sanin yadda ake tsara manhajar WordPress don samun saukin fassararsu
  • Dukkan masu bukatar sanin yadda ake fassara WordPress da kuma yadda ayyukan babbar kungiyar tarjamar take tafiyar da ayyukan ta

Yaushe za’a fara?

Ranar 12 ga watan Nuwamba, 2016, da karfe 12 na dare, agogon UTC
Ga lokutan sauran wurare dabam-dabam na duniya!

Saboda me za muyi wannan bukin?

  • Don kowa ya sarara, kuma don mu san juna
  • Domin mu jawo hankalin wadanda basu san wannan muhimmin aiki na kungiyar fassarar WordPress ba
  • Domin kawo karin haske wajen yadda WordPress ke sarrafa tarjamomi
  • Kuma domin a kara dankon zumunta tsakanin masu hada manhajoji, da masu fassara WordPress

Ta yaya za’a iya shiga?

Kuna iya bada shawarwari akan yadda za’a iya kara samun armashin wannan bukin. Mun yi alkawarin zamu taimaka muku!

Shike nan. Da fatan zamu shafe kokarinmu na baya.

Sai mun ganku!

Mo Ali

Ga wasu muhimman wurare: