Kakakin rundunar sojan sa-kai da ke iko da gabashin Libya, ya ce sun kame gundumar Ganfouda, wadda ke Benghazi, birni na biyu mafi girma a kasar, daga mayaka masu ikirarin Jihadi. Yankin shi ne daya daga cikin yankuna na karshe da ake fafata yaki a cikinsu a birnin na biyu mafi girma a