Firayiministan Korea ta Kudu zai yi murabus

Firayiminista Lee Wan Koo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Firayiminista Lee Wan Koo

Firayi Ministan Korea ta Kudu ya nuna zai sauka daga mukamin sa watanni biyu da zabansa da aka yi.

Mista Lee Wan Koo wanda ya sha alwashin kawar da matsalar cin hanci da rashawa, ya na fuskantar matsin lamba a kan ya sauka saboda samunsa dumudumu a badakalar rashawa.

Wani fitattacen da kasuwar daya kashe kansa, Sung Wan-jong ya bar wasiyya da take kunshe da sunayen 'yan siyasa da jami'an gwamnati da ya ce ya basu na goro, ciki har da Firayi Minista Lee.

Firayiminista Lee ya musanta karbar cin hancin, amma duk da haka ya amince ya sauka daga mukaminsa.