Siyasa | 04.05.20112011-05-04 Deutsche Welle Hausa San'ya hannu kan yarjejeniya tsakanin ƙungiyar Hamas dake iko da zirin Gaza da kuma Fatah wanda ke ƙarƙashin jagorancin Mahmud Abbas wani ci gaba ne na samun masalaha tsakanin bangarorin biyu. Sanya hannu wanda jagoran Hamas Khalid Mashal da shugaban Falastinawa Mahmdu Abbas za su yi, za a yi shine a wani biki a birin Kairo. A Laraban da ta gabata...
Siyasa | 05.01.20112011-01-05 Deutsche Welle Hausa ƙasar Amirka da kuma ƙungiyar Gamayyar Turai na cikin ruƙunin waɗanda suka yi tur da kashe gwamna Salman Taseer da mai tsaron lafiyarsa yayi. Suna masu cewa wannan ba ƙarin koma baya ba ne a Pakistan, kasancewa ya daɗe ya na bayar da gudun mawa wajen tabbatar da ci gaba da kuma kwanciyar hankali a ƙasar. Abin takaicin ma a cewar fadar mulki ta...
Ziyarar shugaban Faransa Nikolas Sarkozy Rwanda2010-02-25 Deutsche Welle Hausa Wannan ziyarar ita ce ta farko da wani shugaban ƙasar ta Faransa ya kai Rwanda tun bayan kisan ƙare dangi a Rwanda a shekarar 1994, saboda haka ake ganin wannan ziyarar ita ce mafi wuya da Nikolas Sarkozy ya taɓa yi. Tun bayan kisan ƙare dangin da ´yan ƙabilar Hutu masu matsanancin ra´ayi suka yiwa ´yan Tutsi da ´yan Hutu masu sassaucin fiye da...
Shekara daya da kama mulkin Obama2010-01-20 Deutsche Welle Hausa A cikin watan janairun shekara ta 2008 ne Barack Obama ya kama aikinsa a fadar mulki ta White House bayan lashe zaɓen da aka gudanar a shekara ta 2007, inda ya riƙa yayata cewar: I zamu iya, wato "Yes we can" da turanci a yaƙinsa na neman zaɓe. To sai dai kuma kimanin shekara ɗaya bayan kama ragamar mulkin an tabbatar cewa hatta mutum kamar Obama,...
Taimakon Jamus ga kasar Haiti2010-01-14 Deutsche Welle Hausa Gwamnatin ƙasar Jamus ta aika da agaji na Yuro miliyan ɗaya, don bada agajin gaggawa ga waɗanda girgizar ƙasar ya shafa a ƙasar Haiti. A wata wasiƙar da ministan harkokin wajen Jamus Westerwelle ya aika, ya kwatanta abun da wani bala'ine wanda ya zama wajibi gwamnatin Jamus ta kai ɗauki. Usman Shehu Usman na da ci gaban rohoto. An amince da...
Shekara guda bayan kare yakin Gaza2009-12-29 Deutsche Welle Hausa A yayin da mafi yawan mazauna yankin Gaza har yanzu suke fama da matsananciyar wahala sakamakon mamayewa da toshe yankin su da Israila tayi, amma ga mazauna Israila din yakin Gaza abu ne da ya zama tarihi Schlomi Eldar ya kasa mantawa da yakin da ya gudana a yankin Gaza, saboda haka ma ya shirya wani film da zai...
Manufofin ƙetare na shugaba Obama2009-12-10 Deutsche Welle Hausa A yau a birnin Oslo aka baiwa shugaban Amurka Barack Obama lambar yabo ta Nobel bisa yunƙurin da ya nuna na samar da wanzuwar zaman lafiya da lumana a duniya. Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Shugaba Barack Obama tare da shugaban kwamitin bada kyautar yabon ta Nobel Thorbjorn Jagland yayin bikin bada...
Jawabin Obama game da Afghanistan2009-12-02 Deutsche Welle Hausa A martanin daya mayar dangane da alƙawarin tura ƙarin dakaru dubu 30 zuwa ƙasar Afghanistan da shugaba Obama na Amirka ya yi, sakatare janar na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen, ya ce yana da yaƙinin cewar, sauran ƙasashen dake ƙawance da Amirkar zasu bi sahunta wajen ƙara yawan sojojin da suke dasu a ƙasar ta Afghanistan. Tuni...
Sabbin Shugabannin Ƙungiyar Tarayyar Turai EU2009-11-20 Deutsche Welle Hausa A jiya ne ƙungiyar tarrayar turai ta zaɓi sabon shugaban ƙasa na ƙungiyar na farko, muƙamin da aka baiwa Piraiminstan ƙasar Beljium, an kuma zaɓi wanda zai shugabacin harkokin siyasa na ƙetare a ƙungiyar, inda 'yar ƙasar Birtaniya wacce ke riƙe da muƙamin komishiniyar kasuwanci na ƙungiyar EU a halin yanzu. Usman Shehu Usman na ɗauke da ƙarin...
Taɓarɓarewar tsaro a Iraƙi2009-11-05 Deutsche Welle Hausa Watanni uku bayan janyewar dakarun Amurka daga manyan biranen ƙasar Iraq, har yanzu halin da ake ciki na rashin tsaro a ƙasar bai inganta ba. Kusan a kullum sai an kai hare hare da ke halaka mutane da dama. Farin cikin farko bayan sanar da janyewar dakarun na Amurka, yanzu haka ya kau a yankuna da dama, a maimakon haka zai zaman zulumi da fargabar...
Siyasa | 27.08.20112011-08-27 Deutsche Welle Hausa Ƙungiyar tayi wannan furuci ne a wata takardar da Anthony Sani da ke zama kakakin ƙungiyar tuntuɓa ta Dattijan jihohin arewa ya gabatarwa manema...
Siyasa | 26.08.20112011-08-26 Deutsche Welle Hausa A wani abinda ke nuna ƙara dagulewar al'amuran tsaro a Najeriya, an kai mumunan harin bam a hedkwatar Majalisar Ɗinkin Ɗuniya da ke Abuja Najeriya, abinda ya ƙara jefa tsoro a game da hare-haren bam da Najeriyar ke fama da su. Harin bam ɗin da aka kai a hedkwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ya yi kama da wani hari na ƙunar baƙin wake, domin kuwa...
Afirka a Jaridun Jamus | 26.08.20112011-08-26 Deutsche Welle Hausa A haƙiƙa dai halin da ake ciki a Libiya, musamman mamayar fadar mulki ta Tripoli da 'yan tawaye suka yi shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus a wannan makon. To sai dai kuma kamar yadda aka saba ba su yi watsi da al'amuran dake wakana a sauran sassa na nahiyar Afirka ba. Da farko dai jaridar Die Tageszeitung, wadda ta sake waiwayar ƙasar Cote...
Labarai | 26.08.20112011-08-26 Deutsche Welle Hausa El Salvador ta bi sahun wasu ƙasashe na yankin Latine Amirka wajen amincewa da Palesdinu a matsayi ƙasa mai cin gashin kanta. Wannan kuwa ya zo ne a daidai lokacin da wa'adin da yankin na palesdinawan ya...
Siyasa | 25.08.20112011-08-25 Deutsche Welle Hausa Bisa ta bakin babban jami'in ƙungiya a Najeria Eric Gutts dai ƙasar ta faɗa wani irin wadi na tsaka mai wuya musamman ta inda fadar gwamnati ke ci gaba da katsalandan a fannin shari'a ta ƙasar musamman game da batun da ya shafi 'yan siyasa wajen sama da faɗi da dukiyar gwamnati . Eric ya ce ga misali ma'aikatar shari'a ta ƙasa tare da haɗin bakin...
Labarai | 25.08.20112011-08-25 Deutsche Welle Hausa Gwamnatin Faransa ta ba da sanarwar ɗaukar sabbin matakan rufe giɓin kuɗin da take fuskanta da kuma farfaɗo da tattalin arzikin...
Siyasa | 24.08.20112011-08-24 Deutsche Welle Hausa Shugabn na Libiya wadda gwamnatinsa ke daf da rugujewa dai ya umurci magoya bayansa da su ci gaba da gwabzawa da 'yan tawaye babu kakkautawa, har sai sun ga abunda ya ture wa Buzu naɗi. Yini guda bayan da 'yan tawaye suka sanar da samun nasarar kutsawa kofar farko na harabar gidan Gaddafi tare da lalata alamun mulkinsa na shekaru 42, ana ci...
Zamantakewa | 24.08.20112011-08-24 Deutsche Welle Hausa Kampanin Ecotec na ƙasar Jamus dake kare gurɓacewar muhalli ta hanyar tattaro tarkachen shara da robobin ruwan sha tare da ledojin purewater wajan sarrafasu yin nagartattun gine ginen zamani masu ƙarko fiye da na ciminti, ya fara horar da ‘yan Najeria sabbin dabarun gini na fasaha ta hanyar tattaro shara wajan tsara ingantattun gidajen dan shawo...
Labarai | 24.08.20112011-08-24 Deutsche Welle Hausa Bayan da 'yan tawaye suka tilasta masa barin gidansa da ke birnin Tripoli, shugaba Muammar Gadhafi ya lashi takobin ci gaba da yaƙi har sai bayan ransa. Bayan da...
Siyasa | 22.08.20112011-08-22 Deutsche Welle Hausa ' Yan tawaye a ƙasar Libiya na ƙokarin karɓe iko da wasu sansanoni ƙarshe da ke cikin hannu mayaƙan da ke yin biyyaya ga kanal gaddafi;yayin dakuma ƙasashen duniya ke ci gaba da yin marhabin da nasara da yan tawaye suka samu ta shiga birin Tripoli Wasu jama'ar a birnin Tripoli sun kasance ciki anashuwa da farinciki a sakamakon kutsen da yan...
Labarai | 22.08.20112011-08-22 Deutsche Welle Hausa 'Yan tawaye a ƙasar Libiya sun isa a tsakiyar birnin Tripoli inda suke riƙe da wasu sansanoni,wanda kuma ake can ake ci gaba da gwabza ƙazamin fada tsakanin dakarun 'yan tawayen da na kanal Gaddafi. 'Yan tawayen waɗanda...
Labarai | 21.08.20112011-08-21 Deutsche Welle Hausa Majiyoyin ƙabilu daga ƙasar Yemen sun bayyana cewar mutane 11 ne suka mutu sakamakon hare-haren ƙunar baƙin wake guda biyun da ake zargin ƙungiyar alQaidah...
Labarai | 20.08.20112011-08-20 Deutsche Welle Hausa A wannan Asabar ce 'yan tawayen ƙasar Libiya suka yi da'awar cewar sun karɓe cikakken iko da birnin Brega, mai tashar teku, kana suna nausawa kusa da birnin...
Siyasa | 19.08.20112011-08-19 Deutsche Welle Hausa Majalisar kula da harkokin shari'ar Najeriyar dai ta ɗauki wannan mataki ne duk kuwa da ƙarar da Mai Sharia Ayo Salami ya gabatar a kotu yana kalubalantar rahoton kwamitin binciken da majalisar da kafa wanda ya zarge shi da yiwa babban jojin...
Afirka a Jaridun Jamus | 19.08.20112011-08-19 Deutsche Welle Hausa A wannan makon ma dai matsalar yunwa da ta addabi gabacin Afirka ta ci-gaba da ɗaukar hankalin jaridun na Jamus. To sai dai a labarin da ta buga game da ƙasar Zimbabwe jaridar Neue Zürcher Zeitung ta fara ne da cewa: "Shekaru uku bayan sanya hannu kan yarjejeniyar gwamnatin ƙawance tsakanin jam'iyar Zanu-PF ta shugaba Robert Mugabe da jam'iyar MDC...
Siyasa | 18.08.20112011-08-18 Deutsche Welle Hausa Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da majalisar kula da harkokin tattalin arzikin ƙasar. Lamarin...
Shekaru 20 bayan faɗuwar katangar Berlin Deutsche Welle Hausa2009-11-04 Bayan wata ɗaya kacal da kammala bikin samun shekaru 40 da kafa ƙasar Jamus ta Gabas katangar da ta raba birnin Berlin gida biyu ta rushe a ranar bakwai ga watan oktoban shekara ta 1989. Kuma kusan shekara ɗaya bayan haka a daidai ranar uku ga watan oktoba sabbin jihohi biyar da aka sake kafawa a yankin Jamus ta Gabas suka shigga tutar tarayyar...
Amincewar Iran da Shawarar Hukumar IAEA Deutsche Welle Hausa2009-11-03 Daulolin ƙasashe masu ƙarfin tatalin arzikin masna´antu sun sake yin kira ga ƙasar Iran, da ta amince da sharuɗɗan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gindaya mata kan shirin ta na makamashin nukliya. Wannan matsin lambar ta zo ne a yayin da ƙasar Iran tace ta amince da sayan makamashin nukliya kai tsaye daga ƙasashen yamma a mai makon aikawa da...
Rahoton Goldstone Deutsche Welle Hausa2009-10-15 Palasɗinawa da Larabawa sun bayyana rashin amincewar su da shawarar da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayar dake buƙatar Palasɗinawa da Israila su kafa kwamitocin cikin gida domin duba zargin aikata laifukan yaƙin da rahoton majalisar ta ɗinkin duniya ta gabatar. A maimakon haka sun buƙaci babban sakataren majlisar ta ɗinkin...
Obama ya samu lambar yabo ta Nobel Deutsche Welle Hausa2009-10-09 A ranar juma'ar nan ne kwamitin dake bada kyautan Nobel ta Duniya dake Norway ta sanar da sunan shugaban Amirka Barak Obama a matsayin wanda ya lashe kyautan Nobel na zaman lafiya na wannan shekara. Kwamitin ta bada wannan kyautan zaman lafiya ne bisa ƙoƙarin da shugaban na Amirka yake takawa wajen samar da zaman lafiya a Duniya baki ɗaya. Shugaban...
Rikicin Birnin Ƙudus Deutsche Welle Hausa2009-10-07 A jiya talata mahukuntan Isra'ila sun tsare Sheikh Raed Salah, mai tsananin kishin Islama har tsawon sa'o'i da dama. Kuma ko da yake an sake shi daga bisani, amma kuma an hana masa sanya ƙafa a birnin Ƙudus tsawon kwanaki talatin masu zuwa, wai saboda kiran da yayi ga musulmi da su taimaka wajen kare makomar masallacin alAqsa, wanda mahukuntan...
Makomar manufofin Jamus a Afghanistan Deutsche Welle Hausa2009-10-05 A kwanakin baya ne wata kafar yaɗa labaru a Jamus ta ruwaito cewa zaá ƙara yawan dakarun ƙasar a Afghanistan izuwa sojoji 7,000, to amma tuni maáikatar tsaro ta yi watsi da wannan rahoton da cewa jita-jita ne kawai. A saboda haka dai babu wani sauyin alƙibla a dangane da manufofin Jamus a Afghanistan. A yanzu haka dai Jamus na da sojoji...
Matakan CIA na yiwa fursinoni tambayoyi Deutsche Welle Hausa2009-08-25 Daga cikin waɗannan matakai har da barazanar kisan kai da fyaɗe da halaka 'ya'ya ko mata da uwayen fursinonin da lamarin ya shafa. Tuni dai ma'aikatar shari'a ta ƙasar Amurka ta ba da umarnin binciken lamarin dalla-dalla. "Har abada ba zamu ɗauki wani matakin da ka iya zama barazana ga makomar tsaron lafiyar Amurkawa akan hukumar CIA ba. Ba zamu sa...
Husa´o´in soja na Barack Obama Deutsche Welle Hausa2009-08-18 Shugaban Amirka Barak Hussain Obama, yayi kira ga Amirkawa dasu ƙara haƙuri dangane da zaman sojojin ƙasar a Afganistan,tare da cewar aikin wanzar da tsaro da kuma zaman lafiya ba abune da za'a samu cikin ƙanƙanin lokaci ba. A lokacin jawabin da yayi, shugaba Barak Obama ya jajjadawa amirkawa irin ƙoƙarin da Amirkan keyi na yaƙi da wa'yan da ya...
Me ya sa aka canja sunan ƙasar Zayar zuwa Kwango Deutsche Welle Hausa2009-07-18 Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun mai sauraronmu a yau da kullum, Malam Jamilu Abdussalam daga jihar Bauchi a tarayyar Najeriya. Malamin cewa ya yi, wane dalili ne ya sa aka canja sunan ƙasar Zayar zuwa Kwango? Yanzu kenan akwai ƙasashe biyu masu suna Kwango! A gaskiya abin na da rikitarwa! Dafatan za ku yi min cikakken bayani....
Ra'ayin masana game da ziyarar Obama a Ghana Deutsche Welle Hausa2009-07-13 Babban abin da ya fi ɗaukara hankalin jama'ar shi ne kiran da ya yi ga ƙasashen Afirka da su kare mulkin dimokuraɗiyya tare da gudanar da shugabanci na gari da kuma gujewa canja kundin tsarin mulki domin cimma wata buƙata. Kusan dukkanin jawaban da shugaba Obama gabatar a ƙasar Ghana, ba su zo wa mutane a bazata ba, domin kuwa dama an tsammaci...