Siyasa | 04.05.20112011-05-04 Deutsche Welle Hausa San'ya hannu kan yarjejeniya tsakanin ƙungiyar Hamas dake iko da zirin Gaza da kuma Fatah wanda ke ƙarƙashin jagorancin Mahmud Abbas wani ci gaba ne na samun masalaha tsakanin bangarorin biyu. Sanya hannu wanda jagoran Hamas Khalid Mashal da shugaban Falastinawa Mahmdu Abbas za su yi, za a yi shine a wani biki a birin Kairo. A Laraban da ta gabata...
Siyasa | 05.01.20112011-01-05 Deutsche Welle Hausa ƙasar Amirka da kuma ƙungiyar Gamayyar Turai na cikin ruƙunin waɗanda suka yi tur da kashe gwamna Salman Taseer da mai tsaron lafiyarsa yayi. Suna masu cewa wannan ba ƙarin koma baya ba ne a Pakistan, kasancewa ya daɗe ya na bayar da gudun mawa wajen tabbatar da ci gaba da kuma kwanciyar hankali a ƙasar. Abin takaicin ma a cewar fadar mulki ta...
Ziyarar shugaban Faransa Nikolas Sarkozy Rwanda2010-02-25 Deutsche Welle Hausa Wannan ziyarar ita ce ta farko da wani shugaban ƙasar ta Faransa ya kai Rwanda tun bayan kisan ƙare dangi a Rwanda a shekarar 1994, saboda haka ake ganin wannan ziyarar ita ce mafi wuya da Nikolas Sarkozy ya taɓa yi. Tun bayan kisan ƙare dangin da ´yan ƙabilar Hutu masu matsanancin ra´ayi suka yiwa ´yan Tutsi da ´yan Hutu masu sassaucin fiye da...
Shekara daya da kama mulkin Obama2010-01-20 Deutsche Welle Hausa A cikin watan janairun shekara ta 2008 ne Barack Obama ya kama aikinsa a fadar mulki ta White House bayan lashe zaɓen da aka gudanar a shekara ta 2007, inda ya riƙa yayata cewar: I zamu iya, wato "Yes we can" da turanci a yaƙinsa na neman zaɓe. To sai dai kuma kimanin shekara ɗaya bayan kama ragamar mulkin an tabbatar cewa hatta mutum kamar Obama,...
Taimakon Jamus ga kasar Haiti2010-01-14 Deutsche Welle Hausa Gwamnatin ƙasar Jamus ta aika da agaji na Yuro miliyan ɗaya, don bada agajin gaggawa ga waɗanda girgizar ƙasar ya shafa a ƙasar Haiti. A wata wasiƙar da ministan harkokin wajen Jamus Westerwelle ya aika, ya kwatanta abun da wani bala'ine wanda ya zama wajibi gwamnatin Jamus ta kai ɗauki. Usman Shehu Usman na da ci gaban rohoto. An amince da...
Shekara guda bayan kare yakin Gaza2009-12-29 Deutsche Welle Hausa A yayin da mafi yawan mazauna yankin Gaza har yanzu suke fama da matsananciyar wahala sakamakon mamayewa da toshe yankin su da Israila tayi, amma ga mazauna Israila din yakin Gaza abu ne da ya zama tarihi Schlomi Eldar ya kasa mantawa da yakin da ya gudana a yankin Gaza, saboda haka ma ya shirya wani film da zai...
Manufofin ƙetare na shugaba Obama2009-12-10 Deutsche Welle Hausa A yau a birnin Oslo aka baiwa shugaban Amurka Barack Obama lambar yabo ta Nobel bisa yunƙurin da ya nuna na samar da wanzuwar zaman lafiya da lumana a duniya. Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Shugaba Barack Obama tare da shugaban kwamitin bada kyautar yabon ta Nobel Thorbjorn Jagland yayin bikin bada...
Jawabin Obama game da Afghanistan2009-12-02 Deutsche Welle Hausa A martanin daya mayar dangane da alƙawarin tura ƙarin dakaru dubu 30 zuwa ƙasar Afghanistan da shugaba Obama na Amirka ya yi, sakatare janar na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen, ya ce yana da yaƙinin cewar, sauran ƙasashen dake ƙawance da Amirkar zasu bi sahunta wajen ƙara yawan sojojin da suke dasu a ƙasar ta Afghanistan. Tuni...
Sabbin Shugabannin Ƙungiyar Tarayyar Turai EU2009-11-20 Deutsche Welle Hausa A jiya ne ƙungiyar tarrayar turai ta zaɓi sabon shugaban ƙasa na ƙungiyar na farko, muƙamin da aka baiwa Piraiminstan ƙasar Beljium, an kuma zaɓi wanda zai shugabacin harkokin siyasa na ƙetare a ƙungiyar, inda 'yar ƙasar Birtaniya wacce ke riƙe da muƙamin komishiniyar kasuwanci na ƙungiyar EU a halin yanzu. Usman Shehu Usman na ɗauke da ƙarin...
Taɓarɓarewar tsaro a Iraƙi2009-11-05 Deutsche Welle Hausa Watanni uku bayan janyewar dakarun Amurka daga manyan biranen ƙasar Iraq, har yanzu halin da ake ciki na rashin tsaro a ƙasar bai inganta ba. Kusan a kullum sai an kai hare hare da ke halaka mutane da dama. Farin cikin farko bayan sanar da janyewar dakarun na Amurka, yanzu haka ya kau a yankuna da dama, a maimakon haka zai zaman zulumi da fargabar...
Siyasa | 21.07.20112011-07-21 Deutsche Welle Hausa Bisa alada dai shugaba Jammeh na ƙasar ta Gambia ya kan keɓe ranar 22 ga kowanne watan yuli amatsayin ranar da ya kira wai ta yanci, sai dai kuma ta la akari da yadda haƙƙin bil adama ke fuskantar barazana daga mahunkuntan ƙasar, ware wannan rana ya zama tamkar wani nutso da malafa. Shugaban dai ya kan yi amfani da tsauri wajen murƙushe dukkan masu...
Amsoshin takardunku | 21.07.20112011-07-21 Deutsche Welle Hausa Ita dai Yingluck Shinawatra, an haife ta ranar 21 ga watan Juni na shekara 1967 wato yanzu ta na da shekaru 44 kenan a duniya. Ita ce 'yar auta a gidansu cikin 'ya'ya tara da ma´aifinsu Shinawatra ya samu. Kama kanwa ce uwa daya uba daya ,ga tsofan Firaministan Thailand, Takhsin Shinawatra wanda a halin yanzu ke gudun hijira a Dubai tun bayan juyin...
Labarai | 21.07.20112011-07-21 Deutsche Welle Hausa Ƙasar Faransa da Jamus sun ɗauki matsiyi guda kan rikicin basuka na ƙasar Girka, gabanin taron gaggawa na ƙasashen da ke amfani da kuɗin euro da aka...
Siyasa | 20.07.20112011-07-20 Deutsche Welle Hausa Dadaab dake arewacin ƙasar Kenya shi ne sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duk faɗin duniya kuma kusan a kullu-yaumin sai ya karɓi baƙoncin 'yan gudun hijira kimanin dubu ɗaya zuwa dubu biyu daga Somaliya. Suna guduwa ne saboda yunwa a ƙasar, wadda a haƙiƙa ta wargaje kwata-kwata: "A kudancin Somaliya al'amura sun taɓarɓare ta yadda kutsawa...
Labarai | 20.07.20112011-07-20 Deutsche Welle Hausa Ƙungiyar Kwadago a tarayyar Najeriya ta sanar da janye yajin aiki na gargaɗi ga gwamnati da ta shirya gudanarwa a yau laraba. Wannan janye yajin aikin dai ya biyo bayan...
Siyasa | 19.07.20112011-07-19 Deutsche Welle Hausa A yanzu dai an kai ga tambayar: shin me waɗannan hare-hare na jiragen saman yaki da kuma matakan diplomasiya suka kawo wa al'amarin gaba ɗaya? Watanni huɗu bayan hare-haren bama-bamai na farko kan Libya, har yanzu dai halin da ake ciki a ƙasar ta hamada a arewacin Afrika bai canza ba.. A ƙarshen mako jami'an...
Labarai | 19.07.20112011-07-19 Deutsche Welle Hausa A wannan Talatar (19.07.11) firaministan ƙasar Birtaniya David Cameron ke tattauna harkokin kasuwanci da kuma dimoƙraɗiyya tare da hukumomin Najeriya, gabannin ya hanzarta komawa gida Birtaniya...
Siyasa | 18.07.20112011-07-18 Deutsche Welle Hausa Ministocin harkokin waje na ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai da ke gudanar da taro a birnin Brussels na ƙasar Beljium sun yi kira da babbar murya da akawo sauyin gwamnatin Bshar Al-Assad a ƙasar Siriya wacce dakarunta ke ci-gaba da fatatakar al'umma dake yin zanga zangar ƙin jini gwamnati. Tun da farko dai daga cikin matakai na matsin lamba...
Labarai | 18.07.20112011-07-18 Deutsche Welle Hausa Ministocin ƙasashen Turai da ke kula da harkokin waje sun bukaci shugaba Bashar al-Assad na Syriya ya sauka daga karagar mulki, sakamakon gaza shawowa cikin ruwan sanyi rikicin ƙasarsa da ya ɓarke tun watanni...
Labarai | 17.07.20112011-07-17 Deutsche Welle Hausa Masu faɗa a ji tsakanin waɗanda ke bijirewa gwamnatin Siriya, sun girka wata sabuwar majalisa wadda zata ƙalubalanci shugaba Basahr al-Assad. Mambobin adawan waɗanda...
Labarai | 16.07.20112011-07-16 Deutsche Welle Hausa A yunƙurinta na neman sassantawa da ƙungiyar wacce haɗin kan ƙungiyoyin ƙawance a ƙarƙashin jagiorancin Amurka suka tumɓuke a shekarar 2001. A yanzu haka...
Siyasa | 15.07.20112011-07-15 Deutsche Welle Hausa Da farko 'yan hamayya ne suka nuna ɓacin ransu game da shaarar sayarwa da ƙasar Saudiyya tankokin yaƙi kuma a yanzun sai ga wata sabuwa ta kunno kai, inda shugabar gwamnati Angela Merkel tayi wa Angola tayin damarar kwale-kwale don sintirin jami'an tsaron gaɓar tekun ƙasar. Abin tambaya shi ne, mene ne alaƙar wannan cinikin da maganar tabbatar da...
Afirka a Jaridun Jamus | 15.07.20112011-07-15 Deutsche Welle Hausa A wannan makon ne dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kai ziyara ga ƙasashen Afirka da suka haɗa da Kenya da Angola da kuma Najeriya. Hakan ta sanya jaridun na Jamus suka fi ba da la'akari ga ziyarar da kuma manufar da shugabar gwamnatin ta sa gaba. Misali dai jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wadda ta fara da tayin cinikin makamai...
Labarai | 15.07.20112011-07-15 Deutsche Welle Hausa Ministocin harkokin waje daga ƙasashen dake ƙungiyar tuntuɓa kan rikicin Libiya, suna ci gaba da ganawa a birnin Instanbul dake ƙasar Turkiya. Mahalartan da...
Amsoshin takardunku | 14.07.20112011-07-14 Deutsche Welle Hausa An fara gasar cin kofin ƙwallon mata ta duniya a shekara 1991 wato yanzu 20 kenan da su ka gabata.An shirya gasar farko a wanan shekara a ƙasar China, kuma Amurika ta lashe kofin a karon na farko, ta yi karon ƙarshe da ƙasar Nowe aka ci Nowe biyu da ɗ€aya. Ƙasashe 12 ne rak suka halarci gasar shekarar farko. A shekara 1995, ƙasar Sweeden ta ɗauki...
Siyasa | 14.07.20112011-07-14 Deutsche Welle Hausa A juma'ar nan ce dai gwamnatin ta Turkiya za ta gudanar da wani taro game da ƙasar ta Libya wadda ake sa ran ministocin harkokin wajen na ƙasashen da ke ƙungiyar tsaro ta NATO za su hallarta da ma dai na sauran ƙasashe domin tattaunawa da 'yan tawaye game da makomar ƙasar bayan an kawar da gwamnatin shugaba Ghaddafi. Wannan taron da ƙasar ta...
Zamantakewa | 14.07.20112011-07-14 Deutsche Welle Hausa A dai halin da ake ciki yanzu miliyoyin mutane daga ƙasashen gabashin Afirka da suka haɗa da Somaliya da Kenya da Ethiopia da Djibouti da Uganda waɗanda tuni suke fama da rikice rikice sun faɗa wani mawuyacin hali sakamakon bala'in fari. A cikin wata sanarwa da ta fitar hukumar kula da 'yan gudun hijra ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce a watan...
Labarai | 14.07.20112011-07-14 Deutsche Welle Hausa A ƙasar Indiya ana nan ana gudanar da bincike akan hare-haren bom da aka aiwaitar ranar Laraba 13 ga watan...
Labarai | 13.07.20112011-07-13 Deutsche Welle Hausa ƙungiyar Human Right Watch ta shedda cewa 'yan tawaye ƙasar Libiya sun aikata ta'asa da feyade dakuma cin zarafi fararan fula, tare da kwasar ganima a kantuna da shaguna, dakuma ƙona wasu...
Shekaru 20 bayan faɗuwar katangar Berlin Deutsche Welle Hausa2009-11-04 Bayan wata ɗaya kacal da kammala bikin samun shekaru 40 da kafa ƙasar Jamus ta Gabas katangar da ta raba birnin Berlin gida biyu ta rushe a ranar bakwai ga watan oktoban shekara ta 1989. Kuma kusan shekara ɗaya bayan haka a daidai ranar uku ga watan oktoba sabbin jihohi biyar da aka sake kafawa a yankin Jamus ta Gabas suka shigga tutar tarayyar...
Amincewar Iran da Shawarar Hukumar IAEA Deutsche Welle Hausa2009-11-03 Daulolin ƙasashe masu ƙarfin tatalin arzikin masna´antu sun sake yin kira ga ƙasar Iran, da ta amince da sharuɗɗan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gindaya mata kan shirin ta na makamashin nukliya. Wannan matsin lambar ta zo ne a yayin da ƙasar Iran tace ta amince da sayan makamashin nukliya kai tsaye daga ƙasashen yamma a mai makon aikawa da...
Rahoton Goldstone Deutsche Welle Hausa2009-10-15 Palasɗinawa da Larabawa sun bayyana rashin amincewar su da shawarar da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayar dake buƙatar Palasɗinawa da Israila su kafa kwamitocin cikin gida domin duba zargin aikata laifukan yaƙin da rahoton majalisar ta ɗinkin duniya ta gabatar. A maimakon haka sun buƙaci babban sakataren majlisar ta ɗinkin...
Obama ya samu lambar yabo ta Nobel Deutsche Welle Hausa2009-10-09 A ranar juma'ar nan ne kwamitin dake bada kyautan Nobel ta Duniya dake Norway ta sanar da sunan shugaban Amirka Barak Obama a matsayin wanda ya lashe kyautan Nobel na zaman lafiya na wannan shekara. Kwamitin ta bada wannan kyautan zaman lafiya ne bisa ƙoƙarin da shugaban na Amirka yake takawa wajen samar da zaman lafiya a Duniya baki ɗaya. Shugaban...
Rikicin Birnin Ƙudus Deutsche Welle Hausa2009-10-07 A jiya talata mahukuntan Isra'ila sun tsare Sheikh Raed Salah, mai tsananin kishin Islama har tsawon sa'o'i da dama. Kuma ko da yake an sake shi daga bisani, amma kuma an hana masa sanya ƙafa a birnin Ƙudus tsawon kwanaki talatin masu zuwa, wai saboda kiran da yayi ga musulmi da su taimaka wajen kare makomar masallacin alAqsa, wanda mahukuntan...
Makomar manufofin Jamus a Afghanistan Deutsche Welle Hausa2009-10-05 A kwanakin baya ne wata kafar yaɗa labaru a Jamus ta ruwaito cewa zaá ƙara yawan dakarun ƙasar a Afghanistan izuwa sojoji 7,000, to amma tuni maáikatar tsaro ta yi watsi da wannan rahoton da cewa jita-jita ne kawai. A saboda haka dai babu wani sauyin alƙibla a dangane da manufofin Jamus a Afghanistan. A yanzu haka dai Jamus na da sojoji...
Matakan CIA na yiwa fursinoni tambayoyi Deutsche Welle Hausa2009-08-25 Daga cikin waɗannan matakai har da barazanar kisan kai da fyaɗe da halaka 'ya'ya ko mata da uwayen fursinonin da lamarin ya shafa. Tuni dai ma'aikatar shari'a ta ƙasar Amurka ta ba da umarnin binciken lamarin dalla-dalla. "Har abada ba zamu ɗauki wani matakin da ka iya zama barazana ga makomar tsaron lafiyar Amurkawa akan hukumar CIA ba. Ba zamu sa...
Husa´o´in soja na Barack Obama Deutsche Welle Hausa2009-08-18 Shugaban Amirka Barak Hussain Obama, yayi kira ga Amirkawa dasu ƙara haƙuri dangane da zaman sojojin ƙasar a Afganistan,tare da cewar aikin wanzar da tsaro da kuma zaman lafiya ba abune da za'a samu cikin ƙanƙanin lokaci ba. A lokacin jawabin da yayi, shugaba Barak Obama ya jajjadawa amirkawa irin ƙoƙarin da Amirkan keyi na yaƙi da wa'yan da ya...
Me ya sa aka canja sunan ƙasar Zayar zuwa Kwango Deutsche Welle Hausa2009-07-18 Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun mai sauraronmu a yau da kullum, Malam Jamilu Abdussalam daga jihar Bauchi a tarayyar Najeriya. Malamin cewa ya yi, wane dalili ne ya sa aka canja sunan ƙasar Zayar zuwa Kwango? Yanzu kenan akwai ƙasashe biyu masu suna Kwango! A gaskiya abin na da rikitarwa! Dafatan za ku yi min cikakken bayani....
Ra'ayin masana game da ziyarar Obama a Ghana Deutsche Welle Hausa2009-07-13 Babban abin da ya fi ɗaukara hankalin jama'ar shi ne kiran da ya yi ga ƙasashen Afirka da su kare mulkin dimokuraɗiyya tare da gudanar da shugabanci na gari da kuma gujewa canja kundin tsarin mulki domin cimma wata buƙata. Kusan dukkanin jawaban da shugaba Obama gabatar a ƙasar Ghana, ba su zo wa mutane a bazata ba, domin kuwa dama an tsammaci...