Siyasa | 04.05.20112011-05-04 Deutsche Welle Hausa San'ya hannu kan yarjejeniya tsakanin ƙungiyar Hamas dake iko da zirin Gaza da kuma Fatah wanda ke ƙarƙashin jagorancin Mahmud Abbas wani ci gaba ne na samun masalaha tsakanin bangarorin biyu. Sanya hannu wanda jagoran Hamas Khalid Mashal da shugaban Falastinawa Mahmdu Abbas za su yi, za a yi shine a wani biki a birin Kairo. A Laraban da ta gabata...
Siyasa | 05.01.20112011-01-05 Deutsche Welle Hausa ƙasar Amirka da kuma ƙungiyar Gamayyar Turai na cikin ruƙunin waɗanda suka yi tur da kashe gwamna Salman Taseer da mai tsaron lafiyarsa yayi. Suna masu cewa wannan ba ƙarin koma baya ba ne a Pakistan, kasancewa ya daɗe ya na bayar da gudun mawa wajen tabbatar da ci gaba da kuma kwanciyar hankali a ƙasar. Abin takaicin ma a cewar fadar mulki ta...
Ziyarar shugaban Faransa Nikolas Sarkozy Rwanda2010-02-25 Deutsche Welle Hausa Wannan ziyarar ita ce ta farko da wani shugaban ƙasar ta Faransa ya kai Rwanda tun bayan kisan ƙare dangi a Rwanda a shekarar 1994, saboda haka ake ganin wannan ziyarar ita ce mafi wuya da Nikolas Sarkozy ya taɓa yi. Tun bayan kisan ƙare dangin da ´yan ƙabilar Hutu masu matsanancin ra´ayi suka yiwa ´yan Tutsi da ´yan Hutu masu sassaucin fiye da...
Shekara daya da kama mulkin Obama2010-01-20 Deutsche Welle Hausa A cikin watan janairun shekara ta 2008 ne Barack Obama ya kama aikinsa a fadar mulki ta White House bayan lashe zaɓen da aka gudanar a shekara ta 2007, inda ya riƙa yayata cewar: I zamu iya, wato "Yes we can" da turanci a yaƙinsa na neman zaɓe. To sai dai kuma kimanin shekara ɗaya bayan kama ragamar mulkin an tabbatar cewa hatta mutum kamar Obama,...
Taimakon Jamus ga kasar Haiti2010-01-14 Deutsche Welle Hausa Gwamnatin ƙasar Jamus ta aika da agaji na Yuro miliyan ɗaya, don bada agajin gaggawa ga waɗanda girgizar ƙasar ya shafa a ƙasar Haiti. A wata wasiƙar da ministan harkokin wajen Jamus Westerwelle ya aika, ya kwatanta abun da wani bala'ine wanda ya zama wajibi gwamnatin Jamus ta kai ɗauki. Usman Shehu Usman na da ci gaban rohoto. An amince da...
Shekara guda bayan kare yakin Gaza2009-12-29 Deutsche Welle Hausa A yayin da mafi yawan mazauna yankin Gaza har yanzu suke fama da matsananciyar wahala sakamakon mamayewa da toshe yankin su da Israila tayi, amma ga mazauna Israila din yakin Gaza abu ne da ya zama tarihi Schlomi Eldar ya kasa mantawa da yakin da ya gudana a yankin Gaza, saboda haka ma ya shirya wani film da zai...
Manufofin ƙetare na shugaba Obama2009-12-10 Deutsche Welle Hausa A yau a birnin Oslo aka baiwa shugaban Amurka Barack Obama lambar yabo ta Nobel bisa yunƙurin da ya nuna na samar da wanzuwar zaman lafiya da lumana a duniya. Bildunterschrift: Großansicht des Bildes mit der Bildunterschrift: Shugaba Barack Obama tare da shugaban kwamitin bada kyautar yabon ta Nobel Thorbjorn Jagland yayin bikin bada...
Jawabin Obama game da Afghanistan2009-12-02 Deutsche Welle Hausa A martanin daya mayar dangane da alƙawarin tura ƙarin dakaru dubu 30 zuwa ƙasar Afghanistan da shugaba Obama na Amirka ya yi, sakatare janar na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO Anders Fogh Rasmussen, ya ce yana da yaƙinin cewar, sauran ƙasashen dake ƙawance da Amirkar zasu bi sahunta wajen ƙara yawan sojojin da suke dasu a ƙasar ta Afghanistan. Tuni...
Sabbin Shugabannin Ƙungiyar Tarayyar Turai EU2009-11-20 Deutsche Welle Hausa A jiya ne ƙungiyar tarrayar turai ta zaɓi sabon shugaban ƙasa na ƙungiyar na farko, muƙamin da aka baiwa Piraiminstan ƙasar Beljium, an kuma zaɓi wanda zai shugabacin harkokin siyasa na ƙetare a ƙungiyar, inda 'yar ƙasar Birtaniya wacce ke riƙe da muƙamin komishiniyar kasuwanci na ƙungiyar EU a halin yanzu. Usman Shehu Usman na ɗauke da ƙarin...
Taɓarɓarewar tsaro a Iraƙi2009-11-05 Deutsche Welle Hausa Watanni uku bayan janyewar dakarun Amurka daga manyan biranen ƙasar Iraq, har yanzu halin da ake ciki na rashin tsaro a ƙasar bai inganta ba. Kusan a kullum sai an kai hare hare da ke halaka mutane da dama. Farin cikin farko bayan sanar da janyewar dakarun na Amurka, yanzu haka ya kau a yankuna da dama, a maimakon haka zai zaman zulumi da fargabar...
Labarai | 27.06.20112011-06-27 Deutsche Welle Hausa Rundunar sojin Najeriya ta ruwaito cewar aƙalla mutane uku ne suka mutu sakamakon wani harin da ake zargin 'yan ƙungiyar Boko-Haramun da ƙaddamar wa a birnin Maiduguri...
Siyasa | 27.06.20112011-06-27 Deutsche Welle Hausa Sai dai ga da yawa daga cikin 'yan ƙasar, ana tafiyar hawainiya. Suna ci-gaba da bore ko dai saboda rashin akin yi ko kuma ba su yarda cewa demokraɗiyyar za ta samar masu wata kyakkyawar makoma ba. To amma akwai masu kyakkyawan fata ciki har da tsohon ɗan adawa Mokhtar Yahyawi. Kimamin watanni biyar kenan da aka hamɓarar da shugaban kama karya Zine...
Amsoshin takardunku | 25.06.20112011-06-25 Deutsche Welle Hausa Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Birtaniya ta Manchester United an girka ta tun shekara 1878 wato yanzu shekaru 133 kenan a wani gari mai suna Trafford kusa da birnin Manchester. Da farko sunan kungiyar Newton Heath, wato suna wani mutumen ne da ya ke daga mutanen da su ka kirkiro gasar cin kofin kwallon kafa Birtaniya a shekara 1982. Sai a shekara 1902 ne,...
Labarai | 25.06.20112011-06-25 Deutsche Welle Hausa Majalisar dattawan jihar New -york ta ƙasar Amirka ta albarkanci ƙudirin dokar yin aure tsakanin jinsi ɗaya da gwamna Andrew Cuomo...
Siyasa | 24.06.20112011-06-24 Deutsche Welle Hausa To sai dai kuma babu wani mizanin da aka bayar dangane da rawar da gasar taka ga tattalin arziƙin ƙasar. Bisa ga dukkan alamu kuwa haka lamarin zai kasance dangane da gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya ta mata a ƙasar daga 26 ga watan Yuni zuwa 17 ga watan Yuli. Yau dai kimanin shekaru biyar ke nan...
Labarai | 24.06.20112011-06-24 Deutsche Welle Hausa Shugabannin ƙasashen Tarayyar Turai sun amince su samar da sabon shirin ceto tattalin arzikin Girka idan majalisar dokokin ƙasar ta zartar da ƙudirin tsuke bakin...
Siyasa | 23.06.20112011-06-23 Deutsche Welle Hausa Shugaban ƙasar Amurika Barack Obama ya bayyana fara janye sojojin ƙasar daga Afganistan kamin ƙarshen shekara da muke ciki. Tun dai shekara ta 2001 ne bayan harin da ƙungiyar Alqa´ida ta afkawa Amurika, hukumomin ƙasar su ka ɗaura ɗamari yaƙi da ta´adanci da yan ta´ada,ta haka ne Amurika ta aika sojoji dubu 100 a ƙasar Afganistan.To saidai har ya...
Labarai | 23.06.20112011-06-23 Deutsche Welle Hausa Ƙungiyar Tarayyar Turai ta bayyana damuwarta dangane da shirin yiwa tsarin zaɓen Senegal gyaran fuska, gabannin zaɓen ƙasar da zai gudana a watan Febrairun shekara mai...
Labarai | 22.06.20112011-06-22 Deutsche Welle Hausa Babban zauren taron Majalisar Ɗinkin Duniya ya sake zaɓan Ban Ki Moon a matsayin sakatare janar na majalisar na wani sabon wa'adin shekaru biyar. A jawabin samun nasarar da yayi - jim kaɗan bayan zaɓen, Ban ya...
Siyasa | 21.06.20112011-06-21 Deutsche Welle Hausa A yayin da aka shiga yini biyu na taron, wanda aka fi sani da Global Media Forum, wakilan kafofin yaɗa labarai da kuma ƙwararrun dake halartar taron na birnin Bonn anan tarayyar Jamus sun yi musayar bayanai game da rawar da kafofin yaɗa labarai za su taka wajen tabbatar da 'yancin bil Adama a nahiyar Afirka, musamman taskar sadarwa da...
Labarai | 21.06.20112011-06-21 Deutsche Welle Hausa A Najeriya, Ƙungiyar da ake yi wa laƙabi da Boko Haram ta sake ƙaddamar da wasu tagwayen hare-hare akan wani caji ofis ɗin 'yan sanda da kuma wani banki a...
Siyasa | 20.06.20112011-06-20 Deutsche Welle Hausa A wannan Litinin 20 ga watan Juni , Radio DW ta buÉa taron da ta saba shiryawa ko wace shekara, wanda aka fi sani da sunan Global Media Forum. A bana ma fiye da mutane 1000 daga sassa daban-daban na duniya su ka halarci wannan taron, inda tsawan yini ukku za su tattanawa game da rawar da kafofin yaÉa labarai ke takawa ta fannin kare...
Labarai | 20.06.20112011-06-20 Deutsche Welle Hausa Ministocin kuɗi na ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai sun amince da shirin tallafa wa ƙasar Girka da ƙarin kuɗaɗen rance a zagaye na biyu domin ceto ƙasar daga matsalar...
Labarai | 19.06.20112011-06-19 Deutsche Welle Hausa Yan tawayen Libya waɗanda ke fafutuka ko ta wane ɓangare domin yanke birnin Tripoli dake zama maƙarfafar Moammar Gaddafi sun arangama da sojojin gwamnati a birnin Nalut dake arewa maso gabashi da...
Labarai | 18.06.20112011-06-18 Deutsche Welle Hausa Sarki Mohammed na Morocco ya yi alƙawarin gudanar da gyaran kundin tsarin mulki wanda zai dace sabuwar alƙibla ta dimokraɗiyya. Sarkin ya faɗi...
Afirka a Jaridun Jamus | 17.06.20112011-06-17 Deutsche Welle Hausa A wannan makon ne dai gwamnatin Jamus ta fitar da sanarwa akan manufofinta dangane da Afrika inda take fatan ƙarfafa dangantakarta da ƙasashen nahiyar a dukkan fannoni na rayuwa. Jaridar Süddeutsche Zeitung tayi nazari akan takardar ta gwamnati ta kuma yi bayani tana mai cewar: "Babban manufar da aka gabatar a wannan takardar dai ita ce cewar Jamus...
Labarai | 17.06.20112011-06-17 Deutsche Welle Hausa Wata takarda da jami'an kotu suka shigar a birnin new York ta yi nuni da cewa tsohon shugaban asusun ba da lamuni na duniya (IMF), Dominique Strauss-Kahn ya...
Shekaru 20 bayan faɗuwar katangar Berlin Deutsche Welle Hausa2009-11-04 Bayan wata ɗaya kacal da kammala bikin samun shekaru 40 da kafa ƙasar Jamus ta Gabas katangar da ta raba birnin Berlin gida biyu ta rushe a ranar bakwai ga watan oktoban shekara ta 1989. Kuma kusan shekara ɗaya bayan haka a daidai ranar uku ga watan oktoba sabbin jihohi biyar da aka sake kafawa a yankin Jamus ta Gabas suka shigga tutar tarayyar...
Amincewar Iran da Shawarar Hukumar IAEA Deutsche Welle Hausa2009-11-03 Daulolin ƙasashe masu ƙarfin tatalin arzikin masna´antu sun sake yin kira ga ƙasar Iran, da ta amince da sharuɗɗan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta gindaya mata kan shirin ta na makamashin nukliya. Wannan matsin lambar ta zo ne a yayin da ƙasar Iran tace ta amince da sayan makamashin nukliya kai tsaye daga ƙasashen yamma a mai makon aikawa da...
Rahoton Goldstone Deutsche Welle Hausa2009-10-15 Palasɗinawa da Larabawa sun bayyana rashin amincewar su da shawarar da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayar dake buƙatar Palasɗinawa da Israila su kafa kwamitocin cikin gida domin duba zargin aikata laifukan yaƙin da rahoton majalisar ta ɗinkin duniya ta gabatar. A maimakon haka sun buƙaci babban sakataren majlisar ta ɗinkin...
Obama ya samu lambar yabo ta Nobel Deutsche Welle Hausa2009-10-09 A ranar juma'ar nan ne kwamitin dake bada kyautan Nobel ta Duniya dake Norway ta sanar da sunan shugaban Amirka Barak Obama a matsayin wanda ya lashe kyautan Nobel na zaman lafiya na wannan shekara. Kwamitin ta bada wannan kyautan zaman lafiya ne bisa ƙoƙarin da shugaban na Amirka yake takawa wajen samar da zaman lafiya a Duniya baki ɗaya. Shugaban...
Rikicin Birnin Ƙudus Deutsche Welle Hausa2009-10-07 A jiya talata mahukuntan Isra'ila sun tsare Sheikh Raed Salah, mai tsananin kishin Islama har tsawon sa'o'i da dama. Kuma ko da yake an sake shi daga bisani, amma kuma an hana masa sanya ƙafa a birnin Ƙudus tsawon kwanaki talatin masu zuwa, wai saboda kiran da yayi ga musulmi da su taimaka wajen kare makomar masallacin alAqsa, wanda mahukuntan...
Makomar manufofin Jamus a Afghanistan Deutsche Welle Hausa2009-10-05 A kwanakin baya ne wata kafar yaɗa labaru a Jamus ta ruwaito cewa zaá ƙara yawan dakarun ƙasar a Afghanistan izuwa sojoji 7,000, to amma tuni maáikatar tsaro ta yi watsi da wannan rahoton da cewa jita-jita ne kawai. A saboda haka dai babu wani sauyin alƙibla a dangane da manufofin Jamus a Afghanistan. A yanzu haka dai Jamus na da sojoji...
Matakan CIA na yiwa fursinoni tambayoyi Deutsche Welle Hausa2009-08-25 Daga cikin waɗannan matakai har da barazanar kisan kai da fyaɗe da halaka 'ya'ya ko mata da uwayen fursinonin da lamarin ya shafa. Tuni dai ma'aikatar shari'a ta ƙasar Amurka ta ba da umarnin binciken lamarin dalla-dalla. "Har abada ba zamu ɗauki wani matakin da ka iya zama barazana ga makomar tsaron lafiyar Amurkawa akan hukumar CIA ba. Ba zamu sa...
Husa´o´in soja na Barack Obama Deutsche Welle Hausa2009-08-18 Shugaban Amirka Barak Hussain Obama, yayi kira ga Amirkawa dasu ƙara haƙuri dangane da zaman sojojin ƙasar a Afganistan,tare da cewar aikin wanzar da tsaro da kuma zaman lafiya ba abune da za'a samu cikin ƙanƙanin lokaci ba. A lokacin jawabin da yayi, shugaba Barak Obama ya jajjadawa amirkawa irin ƙoƙarin da Amirkan keyi na yaƙi da wa'yan da ya...
Me ya sa aka canja sunan ƙasar Zayar zuwa Kwango Deutsche Welle Hausa2009-07-18 Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun mai sauraronmu a yau da kullum, Malam Jamilu Abdussalam daga jihar Bauchi a tarayyar Najeriya. Malamin cewa ya yi, wane dalili ne ya sa aka canja sunan ƙasar Zayar zuwa Kwango? Yanzu kenan akwai ƙasashe biyu masu suna Kwango! A gaskiya abin na da rikitarwa! Dafatan za ku yi min cikakken bayani....
Ra'ayin masana game da ziyarar Obama a Ghana Deutsche Welle Hausa2009-07-13 Babban abin da ya fi ɗaukara hankalin jama'ar shi ne kiran da ya yi ga ƙasashen Afirka da su kare mulkin dimokuraɗiyya tare da gudanar da shugabanci na gari da kuma gujewa canja kundin tsarin mulki domin cimma wata buƙata. Kusan dukkanin jawaban da shugaba Obama gabatar a ƙasar Ghana, ba su zo wa mutane a bazata ba, domin kuwa dama an tsammaci...