Siyasa | 07.10.2009
Rikicin Birnin Ƙudus
A jiya talata mahukuntan Isra'ila sun tsare Sheikh Raed Salah, mai tsananin kishin Islama har tsawon sa'o'i da dama. Kuma ko da yake an sake shi daga bisani, amma kuma an hana masa sanya ƙafa a birnin Ƙudus tsawon kwanaki talatin masu zuwa, wai saboda kiran da yayi ga musulmi da su taimaka wajen kare makomar masallacin alAqsa, wanda mahukuntan Isra'ilar ke gani tamkar wani yunƙuri ne na rura wutar wani sabon rikici...Ahmad Tijani Lawal na da sauran rahoto
Bayan tsare sheikh Raed Salah na gajeren lokaci da mahukuntan Isra'ilar suka yi, a yanzun ana fagabar ɓillar wani sabon rikici tsakanin Musulmi da Yahudawa a kewayen Aqsa, yankin da dake da tsarki ga dukkan sassan biyu, kamar dai yadda jaridar Ma'ariv ta nunar. Hali na zaman ɗarɗar da ake ciki ka iya yin tasiri ba ma kawai akan Larabawan Isra'ila ba, har ma da Palasɗinawa a yankunan dake ƙarƙashin mamayen Isra'ila.. A dai yammacin jiya talata wata ƙaramar kotu a birnin Ƙudus ta saki shugaban wata ƙungiyar Musulmin Isra'ila bayan tsare shi da aka yi har tsawon sa'o'i huɗu. Duk da zargin ga mahukuntan Isra'ila ke yi masa na neman ta da zaune tsaye, saboda kiran da yayi wa musulmi da su ba da gudummawa domin kare makomar masallacin Aqsa, sheikh Raed Salah ya ce har yau yana nan daran da ƙau kan bakansa.
Duk wani mai basira ya san cewar masallacin Aqsa ne ya fi fuskantar barazana dangane da mamayen Isra'ila."
Akwai da da yawa daga 'yan siyasar Isra'ilar dake yin kira da a haramta ƙungiyar ta Musulmi da sheikh Raed Salah ke jagoranta. An saurara daga ministan yaɗa labarai na Isra'ilar Edelstein, ɗan jam'iyyar Likud, mai zazzafan ra'ayin mazan-jiya yana mai cewar wai wajibi ne duk wata gwamnati ta demoƙraɗiyya ta kasance tana da ikon kare kanta daga abokan gabarta. Amma a nasa ɓangaren tsofon ministan tsaron Isra'ila Avi Dichter, ɗan jam'iyyar adawa ta Kadima ya danganta rikicin na baya-bayan nan a birnin Ƙudus da rarrabuwar da ake fama da ita tsakanin ƙungiyoyin Palasɗinawa na Hamas da Fatah. Ga alamu dukkan ƙungiyoyin guda biyu zasu shiga zaɓe shekara mai zuwa kuma a sakamakon haka suke ƙoƙarin yin amfani da birnin Ƙudus don neman goyan baya. A yau laraba sai da Dichter yayi bayani ta gidan rediyon Isra'ilar yana mai faɗi cewar:
"Sheikh Raed Salah kawai ɗan amshin shata ne a wannan matsala. Ana iya cewa ma yana mai ɗoki ne da murna a game da abubuwan dake faruwa tsakanin mahukuntan Palasɗinawa da ma ƙungiyar Hamas. Ka da fa a manta cewar dukkan sassan biyu na shirye-shiryen shiga zaɓe kuma ba wani batun da ya fi jan hankali kamar maganar Ƙudus da masallacin Aqsa, wanda dukkansu biyu wato Hamas da Fatah ke neman yin amfani da shi don neman goyan baya. Shi kuma Sheikh Raed Salah ya zama tamkar ɗan amshi ne a wannan batu."
A nata ɓangaren hukumar Palasɗinu ta zargi Isra'ila da rura wutar rikicin da ake fuskanta sakamakon matakinta na hana wa Musulmin dake ƙasa da shekaru hamsin na haifuwa damar halartar salla a masallacin Aqsa. Tsofon P/M Ahmad Kurei ya ce birnin Ƙudus na fuskantar wata barazanar da bai taɓa fuskantar irin shigenta ba tun bayan shekara ta 1967. Gwamnatin Amurka tayi kira ga Isra'ila da Palasɗinawa da su nuna halin sanin ya kamata. A kuma yammacin yau laraba ne ake sa ran saukar mashawarcin Amurka Mitchell a Isra'ila a wani sabon yunƙuri na sake farfaɗo da shawarwarin zaman lafiyar yankin gabas ta tsakiya.
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita:Zainab Mohammed