Shugaba Muhammar Ƙaddafi ya cika shekaru 40 kan karagar mulki2009-09-01 Deutsche Welle Hausa Yau ne shugaban ƙasar Libiya Muhammar Ƙaddafi ke cika shekaru 40 daidai da hawa karagar mulki. An haifi shugaba Ƙaddafi a shekara ta 1942. Yana ɗan shekaru 27 a duniya ya hamɓarar da Sarki Idriss, ranar ɗaya ga watan Satumba na shekara ta 1969. Tun daga wannan lokaci, Kalan Ƙaddafi ke cigaba da jagorantar ƙasar Libiya, tare da sa toka sa katsi...
Zaɓukan majalisun jihohi uku a Jamus2009-08-31 Deutsche Welle Hausa A yayin da ya rage makonni huɗu a gudanar da man'yan zaɓukan ƙasar Jamus, babban abokin hamayyar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ya yi ikirarin cewar, zai sami nasara a zaɓukan da za'a yi, bayan koma bayan da jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin ta samu a zaɓukan da aka yi a wasu jihohin ƙasar. Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus...
Baƙin hauren Afirka a Turai2009-08-31 Deutsche Welle Hausa Kimanin makonni uku cir suka yi suna watangaririya kan tekun-bahar rum, inda saba'in da uku daga cikinsu suka yi asarar rayukansu. Wannan maganar ta shafi wasu 'yan gudun hijira ne daga ƙasashen Eritrea da Habasha da Nijeriya ta suka taso daga Libiya a ƙoƙarin shigowa nahiyar Turai a cikin wani ɗan ƙaramin kwale-kwale. Wannan tsautsayin na ɗaya...
Shin ƙasar Misira a nahiyar Afirka take ko Yankin Gabas ta Tsakiya2009-08-31 Deutsche Welle Hausa Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malam Bawa Hamza Azare, Jihar Bauchi a Najeriya. Malam Bawa ya ce; Wai shin ita ƙasar Misira a nahiyar Afirka take ne ko a Yankin Gabas ta Tsakiya? In kuma an ce a Afirka take, to me ya sa kodayaushe ake jin ta, ta yi ruwa ta yi tsaki a cikin harkokin siyasar Yankin Gabas ta Tsakiya? Amsa: Tun...
Shirye-shiryen zaɓen Jihohi uku a Jamus.2009-08-28 Deutsche Welle Hausa Tarayyar Jamus dai ƙasa ce dake manyan jihohi daban-daban guda 16. A ranar lahadi mai zuwa ne za a gudanar da zaɓuɓɓukan majalisu a jihohi guda uku, kana kusan wata guda bayan nan a ranar 27 ga watan satumba mai kamawa a gudanar da zaɓen majalisar wakilai na tarayya. Zaɓuɓɓukan majalisun dai zasu gudana ne a jihohin Saarland, Sachsen da kuma...
Azumin watan Ramadan a Jamus2009-08-28 Deutsche Welle Hausa A ƙarshen mako ne al´umar musulmi a ko-ina cikin duniya suka fara azumin watan Ramadana, ɗaya daga cikin shika-shikan addinin musulunci guda biyar. Ga musulmai mazauna nan Jamus azumin na bana na nufin kama baki na tsawon sa´o´i fiye da 16 a kowace rana. Shin yaya wuraren sayar da abinci da shagunan sayar da kayan abinci na musulmai suke tafiyar da...
Sakamakon ayyukan gwamnatin haɗin gwiwa2009-08-27 Deutsche Welle Hausa A zaɓen da aka gudanar a shekara ta 2005 sai da tsofon shugaban gwamnati Gerhard Schröder yayi kurarin cewar tutur, jami'iyyar SPD ba zata shiga ƙarkashin wata gwamnati da Angela Merkel zata shugabanta ba. Amma lamarin sai ya zo akan akasin haka. Domin kuwa bayan zaɓen an kafa gwamnatin haɗin guiwa ne tsakanin 'yan Social Democrats da 'yan...
Husa´ar ƙirƙiro ƙananan Hotel na matasa ta cika shekaru 1002009-08-27 Deutsche Welle Hausa 26 ga watan Ogusta na shekara ta 2009,kwana ta shi, an cika shekaru 100 daidai, da ƙirƙiro husa´ar nan ta kafa wuraren shaƙatawa na yara matasa a nan ƙasar Jamus, wadda ta bazu a sauran ƙasashen duniya, ta kuma rikiɗa zuwa wani dandalin cuɗe ni in cuɗe ka tsakanin matasa daga ko wane ɓangare. Richard Schirmann na ƙasar Jamus, malamamin...
Giɓin kasafin kuɗi a Tarayyar Jamus2009-08-25 Deutsche Welle Hausa Matsalolin tattalin arziki da Duniya ke fama dashi ya jefa kasafin kudin tarayyara Jamus cikin watanni shidan farko cikin hali mawuyaci. Ofishin ƙididdiga na Tarayyar Jamus da ke birnin Wiesbadenya ruwaito cewar, hakan ya danganta ne da koma bayan kudaɗen shiga da kuma irin ɗumbin kuɗin da gwamnati ta kashe wajen cike giɓi, wanda yawansa...
Kamfar ruwa a Kenya2009-08-25 Deutsche Welle Hausa A wannan unguwa, mutane na fama da tsanannin ƙarancin ruwan sha da na amfanin yau da kullun, inda har matattarar ruwa da gwamnati ta tanadar don amfani a lokacin ƙarancin ruwa ta shanye. A unguwar Kangemi farashin ruwa ya yi tashin gwauron zabbi. Wani saurayi mai sayar da ruwa Paul Paul Mwangi ya ƙara kuɗin bokiti ɗaya na ruwa. "Sule uku na kuɗin...
Matakan CIA na yiwa fursinoni tambayoyi2009-08-25 Deutsche Welle Hausa Daga cikin waɗannan matakai har da barazanar kisan kai da fyaɗe da halaka 'ya'ya ko mata da uwayen fursinonin da lamarin ya shafa. Tuni dai ma'aikatar shari'a ta ƙasar Amurka ta ba da umarnin binciken lamarin dalla-dalla. "Har abada ba zamu ɗauki wani matakin da ka iya zama barazana ga makomar tsaron lafiyar Amurkawa akan hukumar CIA ba. Ba zamu sa...
Ƙidayar jama´a a Kenya2009-08-25 Deutsche Welle Hausa Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 10 da wannan ƙasa dake gabashin Afirka ke ƙidayar jama´arta. Taƙaddamar da ake dai shi ne tambaya game da ƙabilun mutane. Masu sukar lamiri na fargabar cewa ana iya amfani da bayanan a hanyoyin da ba su dace ba. To sai dai gwamnati ta ce tara waɗannan bayanan yana da muhimmanci musamman bisa la´akari da...
Sakin al-Megrahi daga kurkukun Scottland2009-08-24 Deutsche Welle Hausa A wannan makon mai ƙarewa jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne akan afuwar da aka yiwa ɗan ƙasar Libya nan Abdel Basit Mohammad al-Megrahi. A rahoton da ta rubuta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa an saki mutumin da aka same shi da laifin tarwatsa wani jirgin saman Amirka a yankin Lockerbie na Scottland bayan ya shafe...
Afghanistan bayan zaɓe2009-08-21 Deutsche Welle Hausa Alƙalumman da hukumar ta bayar sun yi nuni da cewa kimanin kashi 50 cikin 100 na waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri´a suka sauke wannan farali. Yanzu haka dai ana sasa ran samun sakamakon zaɓen a cikin mako mai zuwa. Ko da yake har yanzu demukuraɗiyya jaririya ce a Afghanistan amma babu tantama game da imanin da ɗaukacin mazauna Kabul babban birnin...
Zaɓen shugaban ƙasar Afghanistan2009-08-20 Deutsche Welle Hausa Cikin ƙuri'ar jin ra'ayi da aka gudanar, shugaba Hamid Karzai shine ke gaba koda yake farin jininsa ya ragu a bayansa kuma tsohon ministan harkokin waje, Abdullah Abdullah. A wannan zaɓe dai idan babu wanda ya samu kashi 50% na ƙuri'u dole ne a sake zaɓe zagaye na biyu. Duk da waɗannan matakan tsaro dai hare haren bam a Kandahar da safiyar yau sun...
Ƙasashe nawa ne suke amfani da kuɗin Euro a Tarayyar Turai2009-08-18 Deutsche Welle Hausa Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun malama Ladi Ma'azu daga birnin Yamai a jamhuriyar Niger. Malama Ladi ta ce, wai shin daga cikin ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai, ƙasashe nawa ne suke amfani da kuɗin Euro, kuma ƙasashe nawa ne ba sa amfani da shi, kuma wane dalili ne ya sa ba sa amfani da shi din? Sannan ina so ku sanar da ni...
Husa´o´in soja na Barack Obama2009-08-18 Deutsche Welle Hausa Shugaban Amirka Barak Hussain Obama, yayi kira ga Amirkawa dasu ƙara haƙuri dangane da zaman sojojin ƙasar a Afganistan,tare da cewar aikin wanzar da tsaro da kuma zaman lafiya ba abune da za'a samu cikin ƙanƙanin lokaci ba. A lokacin jawabin da yayi, shugaba Barak Obama ya jajjadawa amirkawa irin ƙoƙarin da Amirkan keyi na yaƙi da wa'yan da ya...
Alkinta ruwan sha a Jamus2009-08-18 Deutsche Welle Hausa Gwamnatin ƙasar Jamus ta bada matuƙar mahimmanci ta fannin samar da wadattatun ruwan sha ga al´umarta.Saboda haka, hukumomi daga matakin gwamnatin Tarayya, har zuwa ƙananan hukumomi suke bada kulawa ta mussamman ga ruwa. A Bad Honnef kusa da birnin Bonn a nan Tarayya Jamus, akwai cibiya samar da ruwa ga dubunan jama´a dake raye a kewayen...
Iran ta yi belin Clotilde Reiss2009-08-17 Deutsche Welle Hausa Wata sanarwar da Ofishin Jakadancin ƙasar Faransa ya fitar, ya bayyana cewar, Gwamnatin Iran ta bayar da belin wata bafaranshiya - Malamar Makarantar data tsare, bisa zargin tallafawa zanga zangar da 'yan adawa a ƙasar suka yi, bayan zaɓukan shugaban ƙasar da aka yi a ranar sha biyu ga watan Yuni. Ofishin Shugaban ƙasar Faransa, Nikolas Sarkorzy ya...
Ziyarar Hillary Clinton a Liberiya2009-08-14 Deutsche Welle Hausa A cigaban ziyarar ta a ƙasashen Afrika, Sakatariyar harakokin wajen Amurika, Hillary clinton ta isa Laberiya, inda ta yabawa shugabar ƙasar Ellen Johnson Searlef ƙoƙarin da take, na daidaita ƙasar bayan yaƙin sama da shekaru goma, da ta yi fama da shi. Dubban...
Rahotan shekara-shekara na Amnesty.2009-05-28 Deutsche Welle Hausa Ƙungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta fitar da rahotanta na shekara-shekara wanda ke bayyana halin ƙunci na talauci da duniya ke ciki da ƙaruwar take hakkokin jama'a a sassa daban-daban na duniya. Matsalar tattalin arziki da Duniya ke ciki, yana barazana wa rayukan mutane kimanin miliyan 90 waɗanda ke fama da matsanancin...
Fafaroma a yankin gabas ta tsakiya.2009-05-13 Deutsche Welle Hausa A ci gaba ziyarar da yake yi da nufin ƙarƙafa matakin tuntubar juna tsakanin mabiya addinai daban daban a yankin gabas ta tsakiya, Fafaroma Benedict na goma sha shidda ya yi kira ga samar da 'yan tacciyar ƙasa ga Falasdinawa. A wannan larabar ce Fafaroma Benedict na goma sha shidda, ya buƙaci samar da 'yan tacciyar ƙasa ta Falastinu, kana ya bukaci...
Garambawul a rundunar Amirka dake Afganistan2009-05-12 Deutsche Welle Hausa A wani mataki na ba zata, Amirka ta sauke Janar Mckiernan, daga matsayin babban kommandan sojojinta a ƙasar Afganistan. Sakataran tsaron Amirka Robert Gates ya bayyana labarin cenjin da sunan shugaban ƙasa Barack Obama. Bayan shekara ɗaya kacal da yayi ya na jagorancin rundunar sojojin Amuruka a Afganista Janar David Mckiernan zai sauka. Za a maye...
Bayan zaɓe a Afirka Ta Kudu2009-05-04 Deutsche Welle Hausa A wannan makon ma dai kamar yadda aka saba jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa akan al'amuran nahiyar Afurka, inda misali jaridar Süddeutsche Zeitung ta sake leƙawa Afirka ta Kudu domin duba irin alƙawururrukan da Jacob Zuma yayi wa talakawan ƙasar in har ya ɗare kan karagar shugabanci da kuma irin ƙwarin guiwar dake...
Zaɓe a Afirka Ta Kudu2009-04-28 Deutsche Welle Hausa A wannan makon dai zaɓen Afirka ta Kudu shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus dangane da nahiyarmu ta Afirka. Misali jaridar Süddeutsche Zeitung tayi amfani da wannan dama domin duba halin da mutane ke ciki a yankunan baƙar fata na ƙasar a cikin wani rahoton da ta gabatar ƙarƙashin taken: "Mazaunin 'yan rabbana ka wadata mu"....
Buƙatocin Afirka ga taron G202009-04-01 Deutsche Welle Hausa Babban saƙon ƙasashen Afrika, wanda Prime Ministan Ƙasar Habasha, Meles Zenawi zai gabatar a wajen Taron ƙasashen da suka fi ƙarfin tattalin arziƙi a Duniya na G20, wanda ake farawa wannan Alhamis dai, shine neman yin la'akari da buƙatun Nahiyar wajen ɗaukacin batutuwan da Taron zai zartar. Prime Minista Meles Zenawi, wanda ke jagorantar...
Barack Obama yayi hira da ´yan jarida2009-03-25 Deutsche Welle Hausa A wannan taron manema labarai shugaba Barack Obama ya taɓo batutuwa dabam dabam da suka shafi tattalin arziki, rikicin nukleyar ƙasar Iran. Barack Obama yace gwamnatinsa ta gaji matsaloli a fannoni dabam-dabam na rayuwar Amurikawa ko wane fanni, to saidai akwai haske a yunƙurin da ake a halin yanzu na magance su. Sannan ya kare tsarin kasafin...
Shiga tsakanin da NATO ta yi a yaƙin Kosobo2009-03-24 Deutsche Welle Hausa Shekaru 10 da suka wuce, a rana mai kamar ta yau, wato 24 ga watan Maris,1999. Rundunar sojojin ƙungiyar NATO, ta kaɗɗamar da yaƙi na tsawon sati 11 akan dakarun sojin ƙasar Sabiya, domin su kare kisan ƙare dangin da aka tasamma yi wa ƙabilar Albaniyawa dake zaune a lardin Kosobo. Kuma an kaɗɗamar da yaƙin ne, bayan da yarjejeniyar zaman lafiya ta...
Obama na shirin ganawa da 'yan Taliban2009-03-09 Deutsche Welle Hausa Yanzu an samu canjin manufa a game da yaƙi a ƙasar Afganistan tsakanin yadda tsohuwar gwamanatin Amirka ƙarƙashin Jagorancin tsohon shugaba Bush da kuma sabuwar gwamnatin ƙarƙashin jagorancin sabon shugaba Barack Obama. Tsohon shugaba Bush dai yana ganin cewa, ya zama wajibi ga Amirka ta ci nasara a yaƙin da take yi a Afganistan, to amma tambayar...